Home Labaru Arewa Maso Gabas: Gwamnatin Buhari Za Ta Dawo Da Yan Chibok 112...

Arewa Maso Gabas: Gwamnatin Buhari Za Ta Dawo Da Yan Chibok 112 – Garba

303
0
Garba Shehu, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa
Garba Shehu, Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

Yau ne aka cika shekaru biyar da ‘yan kungiyar Boko-Haram suka yi awon gaba da yan matan makarantar sakandire na garin Chibok da ke jihar Borno.

Kungiyoyi masu zaman kan su, da fittatun mawaka, gwamnatocin kasashe sun nuna alhinin su tare da daukar alkawura domin ganin an kubutar da yan matan.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu  ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi iyakacin kokarin domin ganin ta dawo da wadanan yan mata cikin koshin lafiya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa an sami ci gaba a tattaunawa domin ganin wadanan dalibai sun dawo nan da ba da jimawa ba. Wasu daga cikin ‘yan makarantar sun dawo, a ya yinda zuwa yanzun babu duri’ar sauren yan makarantar 112.