Home Labaru Arangama : An Kashe Mutum Biyar a Tsakanin ‘Ya’Yan Kungiyar Ansaru Da...

Arangama : An Kashe Mutum Biyar a Tsakanin ‘Ya’Yan Kungiyar Ansaru Da ‘Yan-Bindiga a Birnin Gwari

152
0

An sake arangama tsakanin ‘ya’yan kungiyar Ansaru da kuma ‘yan-bindiga a yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari wanda yayi sanadiyyar kashe ‘yan bindiga biyar.

Wasu mazauna garin Damarin sun shaidawa Muryar Amurka cewa, a daren Litinin din makon nan ma sai da ‘yan kungiyar Ansarun su ka kashe ‘yan-bindiga biyar.

Mutanen wadanda su ka nemi a sakaya sunan su bisa dalilan tsaro, sun ce suna fama da hare-haren ‘yan-bindiga a yankin sosai sai dai idan ‘yan kungiyar Ansaru sun shigo garin su kan basu kariya.

Dama dai yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari na fama da hare-haren ‘yan-bindiga na tsawon lokaci sai dai wasu al’ummar garin sun ce duk lokacin da ‘yan kungiyar Ansaru su ka je garin ‘yan-bindigan ba sa samun damar satar mutane da dukiyarsu.

Leave a Reply