Home Labaru APC Ta Zargi PDP Da Shirya Ta Da Hargitsi Don Hana Zaben 2023

APC Ta Zargi PDP Da Shirya Ta Da Hargitsi Don Hana Zaben 2023

102
0

Kwamitin yaƙin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyar PDP da shirin tada hargisti domin hana gudanar da zaben shekara ta 2023.

Daraktan yada labarai na kwamitin Festus Keyamo ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da su ka wallafa a shafin kwamitin na Twitter, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta gayyatar shugabanin jam’iyyar PDP domin amsa tambayoyi.

Ya ce sun lura cikin damuwa cewa, irin kalaman da ke ƙunshe a sanarwar da PDP ta fitar, ƙarara da alama ce da ke nuni da cewa za su kawo hargitsin a lokacin zaɓe, kuma sun samu bayanai masu ƙarfi akan wadanda ke tada hargitsin a wasu sassan Nijeriya.

Festus Keyamo ya ce kiran ya zama wajibi, bayan wata sanarwa da PDP ta fitar a kan “sahihin zabe, wanda ke cewa su na zargin wasu daidaiku na kokarin kawo hargitsi a zaben shekara ta 2023.

Ya ce dole sai PDP ta samar da bayanai dangane da inda aka yi taron da wadanda su ka halarci taron, da kuma sunayen wadanda ke tada hargitsin ta hanyar kai hare-hare a ofisoshin hukumar zabe ta kasa.