Jam’iyyar APC reshen Jihar Akwa Ibom, ta nemi a tsige Ministan Harkokin Neja-Delta Godswill Akpabio daga mukamin sa.
A cikin wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Akwa Ibom da Sakataren sa Ali Dolari da Ben Nwoye su ka sa wa hannu, sun ce ba su ga amfanin Akpabio a kan mukamin ba.
Shugabannin jam’iyyar, sun zargi Akpabio da yin katsalandan a harkokin Hukumar Raya Yankin Neja Delta.
Jam’iyyar APC ta ce Akpabio ya wuce makadi da rawa, inda ya yi shisshigin nada wa hukumar Manajan Darakta, wanda dokar Nijeriya ta haramta a nada shi.
Godswill Akpabio dai ya nada wani makusancin sa mai suna Dakta Cain Ojogboh a matsayain Daraktan riko mai Kula da Kwangiloli alhalin shi likita ne.
Sun ce dokar da ta kafa hukumar raya yanki Neja Delta ta ce, sai kwararren injiniyan da ya san aikin sa kadai za a nada a kan wannan mukami, sannan su ka ce tun farko Akpabio bai cancanci a ba shi mukamin minista ba.