Home Labaru APC Da Wasu Jam’Iyyu Sun Rasa Mambobi Sama Da 30,000 a Jihar...

APC Da Wasu Jam’Iyyu Sun Rasa Mambobi Sama Da 30,000 a Jihar Buhari

48
0

Akalla mutane dubu 30 da 847 su ka sauya sheka daga jam’iyar APC zuwa PDP a jihar Katsina.

‘Yan siyasar da su ka sauya shekar dai sun fito ne daga kananan hukumomin Sandamu da Mai’Adua da ke yankin Daura, a karkashin jagorancin Danjuma Shu’aibu.

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku da Lado, Mustapha Inuwa ya karbi mutanen, yayin da jirgin yakin neman zaben jam’iyyar PDP ya shiga Mai’Adua da Sandamu a ranar Larabar da ta gabata.

Da ya ke jawabi a gaban dandazon mutanen da su ka halarci gangamin, Mustapha Inuwa ya ce daga cikin masu sauya shekar har da fitattu kuma jiga-jigan mutane a karamar hukumar Sandamu.

BUHARI YA UMARCI SOJOJI SU GAMA DA ‘ƳAN BINDIGAN DA SUKA KASHE JAMI’AN TSARO 7 A KADUNA

Bayan ya yi Allah-Wadai da kisan wasu jami’an tsaro na Civil Deffence 7 da ‘yan baindiga su ka yi a jihar Kaduna, Shugaba Buhari ya umarci Jami’an tsaro su gaggauta kamo maharan su kuma hukunta su.