Yara kanana 17 masu watanni 6 zuwa 5 ne, aka tabbatar da cewa sun mutu, sannan kuma wasu dubu 10 suka kamu da cutar kyanda a jihar Borno.
Darakta yaki da yaduwar cututtuka na ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko a jihar Borno, Babagana Abiso, ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema a Maiduguri na jihar Borno.
Abiso, ya ce gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta wajen daukar matakin gudanar da rigakafi ga kananan yara ‘yan kimanin watanni 6 zuwa shekaru 6 a kananan hukumomi 15 domin shawo kan matsalar a jihar Borno.
Ya ce da farko an sami karancin kayayyakin aikin rigakafin, lamarin da ya janyo tsaiku a wasu yankunan da lamarin ya safa.
Daraktan ya ce sun gano gundumomi 8 wadanda matsalar tafi tsanani, sauran kananan hukumomi 12 da suka rage, kuma a kowanne lokaci za su sam rigakafin daga gwamnati.