Home Labaru Annoba: Kwalara Ta Kashe Mutane 75 Cikin Mako Ɗaya A Jihar Katsina

Annoba: Kwalara Ta Kashe Mutane 75 Cikin Mako Ɗaya A Jihar Katsina

52
0

Cutar Amai da Gudawa ta kashe akalla mutane 75 a jihar Katsina cikin mako guda, yayin da aka samu sama da mutane dubu 1 da 500 sabbin kamuwa da cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Yakubu Danja, ya ce ya zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa ƙananan hukumomin jihar 24 daga cikin 34.

Yakubu Danja, ya ce ƙananan hukumomin da cutar ta fi kamari sun hada da Funtua da Charanci da Kankara da Rimi da Sabuwa da Jibia da kuma Kafur.

” Bisa ga sakamakon binciken mu mun gano cewa kashi 67 bisa 100 na waɗanda suka kamu yara matasa ne ƴan shekara 15 zuwa sama sannan kuma maza ne suka fi kamuwa da ita kwalaran.

Ya ce Karamar hukumar Funtua ce ta fi yawan mutanen da su ka kamu da cutar, inda ta ke da mutane 384, sai kuma Karamar Hukumar Sabuwa da ke da mutane 232, Kafur kuma akwai mutane 215, yayin da Charanci ke da mutane 135, Kankara kuma na da mutane71, yayin da Jibiya ke da mutane 69.