Home Labaru Ana Zanga-Zanga A Edo Kan Tashin Farashin Man Fetur

Ana Zanga-Zanga A Edo Kan Tashin Farashin Man Fetur

37
0
Protesters chant and sing solidarity songs as they barricade barricade the Lagos-Ibadan expressway to protest against police brutality and the killing of protesters by the military, at Magboro, Ogun State, on October 21, 2020. - Buildings in Nigeria's main city of Lagos were torched on October 21, 2020 and sporadic clashes erupted after the shooting of peaceful protesters in which Amnesty International said security forces had killed several people. Witnesses said gunmen opened fire on a crowd of over 1,000 people on the evening of October 20, 2020, to disperse them after a curfew was imposed to end spiralling protests over police brutality and deep-rooted social grievances. (Photo by PIUS UTOMI EKPEI / AFP) (Photo by PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images)

Ƙungiyoyin fararen hula a jihar Edo, sun gudanar da zanga-
zanga a birnin Benin domin nuna adawa da karin farashin man
fetur da aka yi baya-bayan nan.

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna su na Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Nijeriya.

Sun ce abin ya na ci masu tuwo a kwarya, inda su ka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci a Nijeriya.

Masu zanga-zangar dai su na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira dubu 8 da Gwamnatin Tarayya ke shirin yi bayan cire tallafin man fetur.

Leave a Reply