Home Labarai An Yi Kisa A Wajen Zaben Fidda Gwani Na PDP A Jihar...

An Yi Kisa A Wajen Zaben Fidda Gwani Na PDP A Jihar Bayelsa

306
0

Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya yi Allah wadai da kisan wani mutum mai suna Michael Isaiah da aka fi sa ni da suna Tompolo.

Lamarin dai ya faru ne, lokacin da jam’iyyar PDP ke gudanar da zaben fidda gwani a mazabar Ogbia da ke
karamar hukumar Ogbia.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kola Oredipe ya sanya wa hannu, ya ce bata-gari ne su ka yi kisan domin tada zaune tsaye da haddasa tashin hankali a zaben fidda gwanin da aka yi a jihar.

Gwamnan, ya yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike a kan lamarin, tare da tabbatar da an kama
wadanda ke da hannu su kuma fuskanci hukunci daidai da laifin su.

Gwanma Diri dai ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin, da jaddada musu zai tabbatar da an hukunta
wadanda suke da hannu a lamarin.

Leave a Reply