Home Labaru An Yi Harbe-Harbe A Jihar Ogun

An Yi Harbe-Harbe A Jihar Ogun

12
0

Rahotanni sun nuna an samu harbe-harbe a wajen taron wani ɓangare na jam’iyyar APC a Jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne a yau Asabar yayin taron zaɓen shugabannin jam’iyyar da wani ɓangare ya shirya ƙarƙashin jagorancin Ɗan Majalisar Wakilai Ibikunle Amosun a fadar basaraken Abeokuta, Alake na Abeokuta.

Rahotannin sun ce duk da cewa babu tabbacin abin da ya haddasa harbe-harben, magoya bayan jam’iyyar sun shiga ruɗani tare da neman mafaka lokacin da wurin ya hautsine.

Sai dai rahotannin sun ce an ci gaba da ayyukan zaɓen bayan jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.