Home Labaru An Yanka Ta Tashi: Kotu Ta Soke Zaben Dino Melaye A...

An Yanka Ta Tashi: Kotu Ta Soke Zaben Dino Melaye A Jihar Kogi

461
0

Kotun sauraron korafin zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha a Kogi ta soke nasarar zaben Sanata Dino Melaye mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawa.

Hukumar zabe ta INEC ne dai ta kaddamar da Dino a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata da aka gudanar a watan Fabrairu, amma Sanata Smart Adeyemi, na jam’iyyar APC ya tunkari kotun zaben domin kalubalantar lamarin.

Sanata Smart Adeyemi

Smart Adeyemi, ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a zaben da suka hada da magudi da yawan kuri’u da suka wuce ka’ida da kuma rashin bin dokar zabe.

Kwamitin mai mutum uku a karkashin jagorancin mai shari’a Chijioke, a wani hukunci da suka zartar a ranar Juma’ar nan 23 ga watan Agusta, sun amince da hujojjin da Smart ya kafa inda suka yi umurnin a soke  zaben.

Bayan yanke wannan hukuncin Sanata Melaye, ya bukaci magoya bayan sa su kwantar da hankalin su, inda ya ce zai daukaka kara zuwa gaba, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Leave a Reply