Gwamnatin jihar Borno, ta wajabta yin lullubi ga ‘yan mata
Musulmai da ke makarantun ta na sakandare a fadin jihar.
Daraktan Kula da Makarantu na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno Bukar Mustapha-Umara, ya ce a ƙarƙashin sabon tsarin, wajibi ne kowace ɗalibar sakandare Musulma ta sa wando da riga da ɗankwali da lullubi a duk makarantar da ta ke.
Ya ce wannan shigar ta zama wajibi ga dukkan ɗalibai mata Musulmi a duk makarantun sakandare da ke fadin Jihar Borno, amma ga ɗalibai Kiristoci mata zaɓi ne.
Daraktan ya kara da cewa, wajibi ne shugabannin makarantun su tabbatar da bin ƙa’idojin sabuwar dokar, wadda za ta fara aiki daga zangon karatu na farkon shekarar karatu ta 2023 zuwa 2024.