Home Labarai An Tsara Zaben 2023 Ta Hanyar Da Ba Kofar Yin Magudi –...

An Tsara Zaben 2023 Ta Hanyar Da Ba Kofar Yin Magudi – Aishatu Dukku

109
0

Shugabar kwamitin zabe ta Majalisar Wakilai A’isha Jibir Dukku, ta ce an tsara zaben shekara ta 2023 ta hanyar da aka toshe duk wata kafa ta yin magudi.

A’ishatu Dukku ta bayyana haka ne, a wani taron wayar da kai ga masu yada labarai na yanar gizo a mazabar ta, dangane da nagartattun hanyoyin yada labaru domin gudanar da zabe a kan doka da oda.

Ta ce ko da wani ya yi karambanin satar akwatin zabe don wargaza sakamako aikin baban-giwa ne, domin na’ura kai tsaye ta ke dauka da kidayar kuri’un da a ka kada.

A’ishatu Dukku, ta ce sabuwar na’urar ta na da tsarin gane mutum ta hanyar hoton sa, ko da kuwa yatsun shi sun sude saboda noma ko wani aikin kwadago.

‘Yar majalisar, ta bukaci ‘yan Nijeriya su fito su jefa kuri’ar su ga duk wanda su ke so ba tare da shakkar rashin adalci ba.