‘Yan Majalisar Dokoki na Jihar Nasarawa, sun zaɓi Ibrahim
Balarabe Abdullahi na jam’iyyar APC a matsayin Shugaban
Majalisar jihar ta bakwai.
Haka kuma, ‘yan majalisar sun zaɓi Yakubu Bala na jam’iyyar PDP a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.
Muƙaddashin akawun majalisar Ibrahim Musa ya sanar da haka, yayin rantsar da ‘yan majalisar ta bakwai a birnin Lafia.
Ya ce an rantsar da ‘yan majalisar ne daidai da damar da Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya bada, wanda ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa.