Home Labaru An Samar Da Dokar Kisa Kan Masu Sace Jama’a A Katsina

An Samar Da Dokar Kisa Kan Masu Sace Jama’a A Katsina

260
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya sanya hannu kan dokar Penal Code da aka yi kwaskwarima wadda ta bayyana satar mutane da shanu a matsayin manyan laifukan da suka cancanci hukuncin kisa.

Dokar ta kuma amince da hukuncin daurin rai da rai ga masu yi wa mata fyade.

Gwamna Masari ya ce, jihar Katsina na fama da matsalar tsaro wannan shi ne abinda ya sa aka yi wa dokokin jihar gyarar fuska.

Kazalika ya yi fatar matakin da gwamnatin dauka a yanzu, zai zama izna ga mutanen da ke da shawa’ar shiga harkar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.

Leave a Reply