Home Labaru Kiwon Lafiya An Sallami Masu Coronavirus 11 Daga Asibiti A Legas

An Sallami Masu Coronavirus 11 Daga Asibiti A Legas

764
0

An sallami mutum 11 daga asibiti bayan sun warke daga cutar Coronavirus a jihar Legas.

Gwamna Babajide Sanwo-olu ya sanar da cewa wadanda warken sun hada da mace 3 da maza 9.

Da yake jinjina wa ma’aikatan lafiya kan aikin yakar annobar coronavirus, Sanwo-Olu ya bayyana farin cikin ganin mutanen sun koma gida bayan sun shafe kwanaki a cibiayr killace masu cutar.

A sakon daya fitar a yammacin Alhamis, gwamnan ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su dage wurin ganin an kawo karshen cutar.

Ya kuma yi kira da ci gaba da yin yin kokari wurin bin shawarwarin kwararru domin dakile yaduwar cutar.

Mutanen da suka warke da cutar sun kuma yi wani bidiyo domin nuna cewa cutar coronavirus ba mutuwa ba ce, amma tana iya kama kowane irin mutum.

Leave a Reply