Home Labaru An Sako Kwamishinan Yada Labaran Jihar Neja

An Sako Kwamishinan Yada Labaran Jihar Neja

73
0
An Sako Kwamishinan Yada Labaran Jihar Neja

Rahotanni daga jihar Neja sun ce, an sako kwamishinan yada labarai Sani Idris da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar.

A ranar Lahadi da ta gabata ne, ‘yan bindiga suka sace Idris a yankin Baban Tunga da ke karamar hukumar Tafa ta jihar.

Mataimaki na musamman ga kwamishinan Iliya Garba ya ba da tabbacin cewa an sako kwamishinan, inda ya ce ‘yan binigar sun sako shi ne ba tare da biyan kudin fansa ba.

Ya ce, suna godiya ga Allah da ya dawo masu da shi da ransa, bayan iyalansa sun dauki nauyin komai tare da rokon Allah.