Wasu Rahotanni na cewa, an saida akalla mutane 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Katsina a matsayin bayi a kasar Burkina faso.
Wata majiya ta ce, an yi garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Kankara, sannan aka saida su ga wata mata a Kwatano, wadda ita kuma ta saida su ga wani mai cinikin bayi a kasar Burkina Faso.
Wata majiya ta ce, tuni mai taimaka wa gwamna Masari na musamman a kan tu’ammali da miyagun kwayoyi da safarar mutane Alhaji Brodo ya tafi Burkina Faso domin tattauna batun sakin mutanen.
Da ya ke tabbatar da lamarin, Brodo ya ce tabbas zai tafi Burkina Faso a karshen makon nan, domin in tabbatar ko mutanen 20 ‘yan asalin jihar Katsina ne bayan ya hadu da wadanda su ka yi garkuwa da su.
You must log in to post a comment.