Rahotanni daga jihar Taraba na cewa, an sace buhunnan
shinkafa da na Masara da kayayyaki na miliyoyin Naira a
wani katafaren dakin ajiyar kaya da ke Jalingo.
Wata majiya ta ce, wasu gungun Matasa ne su ka kai farmaki gidan ajiyar da ke kusa da rundunar doji.
Bayanai sun nuna cewa, katafaren gidan ajiyar kayan abincin mallakin wani dan majalisar jiha ne, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.
Ɗaya daga cikin masu gadin wurin da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce a lokacin da matasan su ka fara haduwa da misalin karfe 11:50 na dare an sanar da sojoji da ‘yan sanda.
Ya ce da isar jami’an tsaro wurin sun yi harbi domin tarwatsa ɓarayin kuma garin haka ne su ka harbe mutane biyu.
Kayayyakin da aka kwashe dai sun hada da daruruwan buhunan Masara da na shinkafa da aka sarrafa a cikin gida, da kuma kayan amfanin gona da su ka hada da taki da maganin kashe kwari.