Home Labaru Ilimi An Kori Daliban Makarantar Sakandare 71 A Jihar Akwa-Ibom

An Kori Daliban Makarantar Sakandare 71 A Jihar Akwa-Ibom

637
0

A kalla dalibai 71 na makarantar sakandaren gwamnati da ke Etoi a karamar hukumar Uyo ta jihar Akwa Ibom ne aka dakatar, sakamakon zargin su da laifin kone makarantar.

Rahotanni sun nuna cewa, wasu daga cikin daliban makarantar da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, sun yanke hukuncin lalata kadarorin makarantar, inda aka gano sun rufe shugaban makarantar na wasu sa’o’i bayan sun hari masu gadin makarantar.

Kwamishinan ilimi na jihar Farfesa Nse Essien ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya zanta da manema labarai, inda ya ce

Za su dakatar da dalibanan kuma babu ranar dawowa, saboda mugun aikin da su ka yi a makarantar.

Ya ce za su yi hakan ne domin tsaftace bangaren, sannan matakin ya zama darasi ga wasu, ya na mai cewa daliban shekarar karshe da ke cikin su ba za su zauna jarabawar kammala sakandare ba, domin bayyana yadda gwamnati ke son hana rashin da’a a makarantu.

An dai dora wa malaman makarantar laifi, saboda yadda su ka ba daliban tarbiya mara kyau, lamarin ya taka rawar gani wajen wannan mugun aiki da su ka yi.

Leave a Reply