Home Labaru Ilimi An Koma Karatu A Jami’Ar Ahmadu Bello

An Koma Karatu A Jami’Ar Ahmadu Bello

124
0

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,
ta sanar da sake bude makarantar domin ci-gaba da gudanar
karatun zango na biyu.

A wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a mujallarta da ke fita lokaci zuwa lokaci, ta ce sakamakon taron gaugawa karo na 523 da majalisar ta gudanar, an bukaci daukacin dalibai su koma domin ci-gaba da karatu daga ranar Litinin, 19 ga watan Yuni na shekara ta 2023.

Idan dai ba a manta ba, daliban jami’ar sun shafe tsawon wata guda su na zaman gida sakamakon yanke wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na jihar Kaduna KEDCO ya yi.

Sai dai bincike ya tabbatar da dawowar wutar lantarkin, lamarin da ake zargin shi ne ya sa aka yi wa daliban kiranyen komawa domin ci-gaba da karatu.

Leave a Reply