Home Labaru An Kashe ‘Yan Daba Uku A Abuja

An Kashe ‘Yan Daba Uku A Abuja

505
0
An Kashe ‘Yan Daba Uku A Abuja

Wasu ‘yan daba 3 sun rasa rayukan su sakamakon wani hari da su ka kai a kauyan Peace da ke Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin karamin fashi da kuma tashin hankali, saboda yadda aka samu asarar dukiya mai dimbin yawa.

Wata majiya ta ce, lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin suka yi wa wasu matasa duka, bayan sun dakile yunkurin fashi da yaran suka yi yunkurin aiwatarwa.

Amma daga bisani ‘yan daban sun shirya gungu guda tare kai farmaki a garin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku daga cikin maharan, da kuma jikkata da dama daga cikin mazauna yankin, kana kuma an kona gidaje da motoci masu yawa.

Kakakin ‘yan sandan birnin tarayy, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike da kuma tsaurara tsaro a yankin.