Wasu ɓatagari sun kai hari cocin Celestial da ke birnin Lokoja na Jihar Kogi, inda su ka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.
Shaidu sun bayyana wa manema labarai cewa, ɓata-garin sun afka cikin cocin ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka bude wuta a kan kiristocin da su ka je yin addu’a.
Tuni dai an kai gawarwakin mutanen biyu Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Lokoja, yayin da wadanda su ka jikkata aka garzaya da su zuwa wani asibiti domin yi masu magani.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar SP Williams Ayah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta tura jami’an ta zuwa yankin domin kamo wadanda su ka kai harin.