Home Home An Kashe Mutum 1 Tare Da Harbe ‘Yan Sanda Biyu A Zanga-Zangar...

An Kashe Mutum 1 Tare Da Harbe ‘Yan Sanda Biyu A Zanga-Zangar Masu Kishin Yarabawa

119
0
Zanga-zangar masu rajin kafa kasar Yarabawa a yankin Ojota na jihar Legas, ta yi sanadiyyar kashe mutum guda tare da harbe jami’an ‘yan sanda biyu.

Zanga-zangar masu rajin kafa kasar Yarabawa a yankin Ojota na jihar Legas, ta yi sanadiyyar kashe mutum guda tare da harbe jami’an ‘yan sanda biyu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Benjamin Hundeyin ya fitar, ya ce an garzaya da jami’an ‘yan sandan da aka harba asibiti domin yi masu magani.

Sanarwar ta ce tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta aike da tawagar jami’anta domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar dai sun afka wa jami’an ‘yan sandan tare da ƙona motoci biyu, sai dai jami’an ‘yan sandan sun tabbatar da kama mutane hudu da ake zargi da hannu a rikicin.

Sanarwar ta ce tuni an maido da doka da oda a yankin, don haka jami’an ‘yan sanda sun bukaci jama’a su koma harkokin su na yau-da-kullum, yayin da rundunar ta ce ta na kan ɗaukar matakai domin hana faruwar makamancin rikicin nan gaba.

Leave a Reply