Home Home An Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Mai Dubu-Dubu A Sakkwato

An Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Mai Dubu-Dubu A Sakkwato

90
0

Rundunar ‘yan sandan Sokoto ta kashe kasurgumin dan bindiga Bello Hantsi da aka fi sani da mai dubu-dubu a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ahmad Rufa’i ya ce jami’ansu sun kuma kwato makamai daga hannun dan bindigar da suka mkashe a karamar hukumar Kware.

Sanarwar da ya fitar ta, Rufa’i ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto Ali Hayatu Kaigama ya ce mai dubu-dubu na daga cikin masu siyar wa sauran ‘yan bindiga makamai.

Haka kuma, sanarwar ta ce babban DPO na yankin Kware da jami’ansa sun je farautar mai dubu-dubu ne a wani daji aka ji alamar motsinsa, kuma yana hangensu sai ya fara harbi domin samu damar tsare wa, amma ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda uka harbe shi, sannan sauran abokansa suka tsere da raunin harbi a jikinsu.

Yanzu haka dai, rundunar ‘yan sandar ta dauko gawarsa, sannan ta samu bindiga kirar AK-47 daya da harsasai 21 a inda aka kashe shi.

Leave a Reply