Hadakar jami’an tsaro sun samu nasarar kama wani kasurgumin mai safarar miyagun makamai, yayin wani sintirin hadin gwiwa a jihohin Kogi da Nassarawa, musamman a kan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi .
Wata sanarwa da kakakin hukumar tsaro ta DSS Peter Afunyaya ya raba wa manema labarai, ta ce jami’an tsaron sun kama Abubakar Muhammad da makamai da harsasai guda 486, da abubuwan fashewa ashirin da hudu, da kudade a cikin wata mota kirar Gulf.
Haka kuma, jami’an tsaron sun kuma kai wani samame a maboyar jagoran ‘yan ta’addan na jihar Kogi mai suna Kabir Bala da ake yi wa lakabi da Okwo, inda shi da sauran mutanen sa su ka bude wa jami’an tsaron wuta, amma nan take su ka maida martani har daga karshe su ka bindige shi.
Sanarwar ta ce an samu bindiga kirar Ak 47, da wasu bindigogi na gargajiya guda shida, da wayoyin salula da layu da wasu sauran abubuwa.














































