Home Labaru An Kama Mutum 3 Sun Yi Wa ’Yar Shekara 12 Fyade A...

An Kama Mutum 3 Sun Yi Wa ’Yar Shekara 12 Fyade A Bauchi

68
0

Wasu mutane hudu sun shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin
su da aikata laifuffuka, ciki kuwa har da wasu uku da ake
zargin sun yi ma wata karamar yarinya fyade a garin Jalam da
ke Karamar Hukumar Dambam a Jihar Bauchi.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar, ta kuma kama wani matashi dan shekaru 27 bisa zargin lalata wata ‘yar shekaru bakwai a Karamar Hukumar Itas Gadau ta jihar.

Masu fyaden da ka kama a Jalam, sun yaudari yarinyar ne lokacin da ta ke tallar Awara a wajen Kasuwar Dambam, kafin daga bisani su ka yi mata fyade daya bayan daya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Bauchi SP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne lokacin da wani likitan da ke aiki a babban asibitin Dambam ya sanar da ‘yan sanda.

Wakil ya ce bincike ya kai ga kama wasu mutanen uku, kuma lokacin da ake yi masu tambayoyi duk wadanda ake zargin sun amsa laifin su.

Leave a Reply