Majalisar dokoki ta Jihar Sokoto, ta sanya hannu a kan wani
kudirin dokar da ke sa-ido a kan tsada da almubazzarancin da
jama’a ke yi a bikin aure.
Kudirin, wanda Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC da Faruk Balle na Jam’iyyar PDP su ka gabatar, sai da aka fara gabatar da shi ga Kwamitin Kula da Al’amurran Addini na majalisar.
Abubakar Shehu, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahoton su a wani zaman farko na ‘yan majalisar kuma daukacin su sun amince ya zama doka.
Kudirin dokar dai ya na bukatar sa-ido a kan almubazzarancin kudi da ake yi yayin bikin aure da taron suna da kaciya da sauran bukukuwa a sassan jihar.
Bayan wata muhawara a zaman farko da mataimakin shugaban majalisar Alhaji Abubakar Magajya jagoran takudirin dokar ya samu amincewar ‘yan majalisar.














































