Home Labaru An Janye Yan Sandan Da Ke Gadin Tsofaffin Jami’An Gwamnati A Nijeriya

An Janye Yan Sandan Da Ke Gadin Tsofaffin Jami’An Gwamnati A Nijeriya

94
0

Hukumar kula da harkokin ‘yan sandan Nijeriya, ta janye
jami’an kwantar da tarzoma da ke aikin kare wasu tsofaffin
jami’an gwamnati, ciki kuwa har da uwargidan tsohon
shugaban kasa A’isha Buhari da Mamman Daura da tsohon
ministan ‘yan sanda Maigari Dingyadi.

Sauran mutanen da abin ya shafa kuma sun haɗa da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da tsohon shugaban majalisar dattawa Iyorchia Ayu.

Rahotanni sun ruwaito wata sanarwa daga helkwatar rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta na cewa umarnin ya fara aiki nan take.

Sanarwar ta kara da cewa, an dauki matakin ne da nufin inganta jami’an ‘yan sandan da ake turawa da kuma tabbatar da yin amfani da kayan aiki yadda ya kamata domin shawo kan kalubalen tsaron da ake fama da shi a Nijeriya.

Leave a Reply