Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An haramta wa motocin bas shiga Kano

Daga Talata ba a yarda motocin bas su shiga jihar Kano ba.

Gwamnatin Kano ta haramta wa motocin bas shiga jihar tare da tsawaita dokar hana fita na mako 2 don guje wa cutar coronavirus

Gwamnatin jihar Kano ta kara sanya dokar hana fita da ta sanya a fadin jihar domin dakile cutar coronavirus.

Gwamnatin ta kuma haramta wa motocin bas masu daukar fasinjoji da yawa shiga jihar daga ranar Talata.

Kwamishinan Yada Labarai, Muhammad Garba ya ce, an haramta wa bas-bas shiga jihar ne saboda yadda suke daukar mutane fiye da kima a daidai lokacin da ake bukatar ba da tazara a tsakanin mutane domin guje wa yada cutar coronavirus.

Ya ce karin wa’adin mako 2 da gwamnatin ya ki a kan dokar hana fitar da ta fara sanyawa a ranar 25 ga watan Maris, zai fara aiki ne daga ranar Talata 7 ga watan Afrilun da Muke ciki.

Muhammad Garba ya ce tsawaita dokar zama a gidan na daga matakan da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ke dauka na kauce wa bullar cutar coronavirus a jihar.

Ya kuma bukaci jama’ar jihar da su bi hanyoyin kariya da jami’an lafiya da masana ke bayarwa, domin ganin ba a samu bullar cutar a jihar ba.

Jihar Kano na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da har yanzu ba a samu bullar cutar coronavirus ba. Gwamantin jihar ta ce tana aiki kan jiki kan karfi domin tabbatar da ganin cutar ba ta shiga jihar ba.

Jihohi da dama a Najeriya sun sanya dokar hana fita tare da rufe iyakokinsu a kokarinsu na ganin cutar ba ta kara yaduwa ba a kasar da kawo yanzu fiye da mutum 220 ke dauke da cutar.

Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ayyana cutar COVID-19, wadda ta fara bulla a kasar China a watan Disamban shekarar 2019, a matsayin annoba a duniya.

Kawo yanzu cutar ta yadu zuwa kasashe fiye da 100, inda ta kama sama da mutum miliyan 1, da daukan dubban rayuka.

Duk da cewa wasu dubban mutane da suka kamu da cutar sun warke, amma har yanzu cutar COVID-19 ba ta wani sanannen magani.

Exit mobile version