Home Labarai An Gurfanar Da Sojan Da Ya Danne Naira Miliyan 20 Da Aka...

An Gurfanar Da Sojan Da Ya Danne Naira Miliyan 20 Da Aka Yi Kuskuren Tura Wa Bankin Sa

94
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta maka wani
jami’in sojan sama mai suna Haruna Samuel a babbar kotun Kaduna, sakamakon kalmashe wasu kudade naira miliyan 20 da ma’aikatar sa ta yi kuskuren turawa a asusun ajiyar san a banki.

Haruna Samuel, ya ce tabbas ya ga kudin sun shiga asusun
bankin sa, amma su na shiga ya tattara su ya cigaba da hidimar
gaban sa, ganin cewa kudin daga wurin aikin sa ne a ka turo.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ya ce abin da
Samuel ya yi sata ce kuma ya saba wa tsarin dokar kasa.

A karshe Lauyen Haruna Samuel S.A Yahaya ya nemi kotun ta
bada belin wanda ya ke karewa, inda aka dade shari’ar zuwa
ranar 10 ga watan Maris domin ci-gaba da saurare.