Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An Ceto Daliban Jami’ar JOS 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Filato, ta ceto daliban Jami’ar Jos guda 6 daga cikin 7 da aka yi garkuwa da su a daren ranar Litinin da ta gabata.

Kakakin rundunar DSP Alfred Alabo ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin Jos, inda ya ce rundunar ta ceto dalibai 5, yayin da dalibi ya kufce daga hanun masu garkuwar a wajen da su ka boye su.

Ya ce a halin yanzu daliba 6 daga cikin 7 da aka yi garkuwa da su sun kubuta daga hanun ‘yan ta’addan.

DSP Alfred Alabo, ya ce wannan ya faru ne sakamakon matakin da Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Filato Bartholomew Onyeka ya dauka cikin gaugawa bayan faruwar al’amarin tare da hadin kan iyayen daliban.

Exit mobile version