Rahotanni sun tabbatar da cewa, an dawo da jigilar sauka da tashin jirage a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, bayan ma’aikatan sufurin jiragen sama sun hana sauka da tashin jirage a filin jirgin saboda takaddamar da aka samu tsakanin mahukuntan kula da sufuri jirage a Nijeriya.
Wani jami’i a filin jirgin, ya ce ma’aikatan sun hana tashin jiragen kamfanin sufurin jiragen sama na AZMAN da Max Air zuwa Abuja, inda su ka sa aka sauke fasinjojin da su ka riga su ka hau jirgi.
Matakin kuwa ya rutsa da wasu gwamnoni da ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa da wasu manyan mutane da ke filin jirgin, inda su ka ta kokarin ganin an sasanta domin ci-gaba da jigilar fasinja.
Hukumar gudanarwa ta Filin Jirgi na Malam Aminu Kano sun fara takun saka ne, bayan Kungiyar Ma’aikatan da ke ba Jiragen Sama Hannu sun dakatar da ayyukkan su, sakamakon yanke wutar lantarki a filin jirgin da gidan ma’aikatan sa saboda rashin biyan kudin wutar lantarki.
You must log in to post a comment.