Gwamnatin jihar Zamfara, ta amince da sake bude kananan hukumomin Gummi da Anka da Bukkuyum da ta rufe saboda dalilai na tsaro.
A wata Sanawa da kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ya fitar, ta ce umurnin budewar ta shafi kasuwanni da manyan hanyoyi a kananan hukumomin jihar.
Sai dai sanarwar ta bukaci jama’a su kasance masu bin doka da oda.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kananan hukumomin domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro.

