Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An Ɗage Haramcin Amfani Da Babura Masu Ƙafa Biyu A Kudancin Jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe, ta sanar da ɗage haramcin amfani da babura a kudancin jihar.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba gwamnan jihar shawara ta fuskar tsaro Janar Ɗahiru Abdussalam, ta ce ƙananan hukumomin da aka ɗage haramcin sun haɗa da Fika da Fune da Nangere da Potiskum da Bade da Machina da Nguru da Jakusko, da Karasuwa da kuma Yusufari.

Sai dai gwamnatin jihar ta sa wasu sharudɗa ga masu amfani da baburan da su ka haɗa da amfani da su kawai daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma sannan banda goyo.

An kuma ba su umarnin yin rijistar baburan su, sannan za su yi zirga-zirga ne a iya ƙananan hukumomin da su ke banda tsallakawa wata ƙaramar hukuma.

Exit mobile version