Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An Ƙaddamar Da Shirin Rage Mutuwar Mata Masu Ciki A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin magance matsalar mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara a Nijeriya.

Ana sa ran shirin zai rage matsalar mace-macen mata da kananan yara da kashi 25 cikin 100 nan da shekara ta 2025, kuma ana sa ran zai shafi mutane miliyan 2 da dubu 300.

An dai yi ƙiyasin cewa, za a kashe dala milliyan 4 da dubu 35 wajen aiwatar da shirin, kuma ana sa ran ƙungiyar Rotary ce za ta bada tallafin.

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya, ya nuna Nijeriya ce ke da kashi ɗaya cikin huɗu na mace-macen mata da kananan yara da ake samu a faɗin duniya. Rahoton ya ce, abubuwan da su ka fi yin sanadiyyar rayukan matan sun haɗa da zubar da jini bayan haihuwa, da cutar jijjiga da kuma matsalolin da ake fuskanta lokacin zubar da ciki, sai kuma gudawa da malariya da ke sanadin mutuwar kananan yara da dama.

Exit mobile version