Home Labaru Amurka Za Ta Bada Tukuicin Dala Miliyan 7 Ga Wanda Ya...

Amurka Za Ta Bada Tukuicin Dala Miliyan 7 Ga Wanda Ya Bayyana Ida Shekau Ya Ke

530
0
Amurka Za Ta Bada Tukuicin Dala Miliyan 7 Ga Wanda Ya Bayyana Ida Shekau Ya Ke
Amurka Za Ta Bada Tukuicin Dala Miliyan 7 Ga Wanda Ya Bayyana Ida Shekau Ya Ke

Sashin shari’a na kasar Amurka ya ce an ware kyautar Dalla miliyan 7 kwatankwacin fiye da Naira biliyan 2 ga duk wanda ya bada bayanai da su ka yi sanadiyyar kama shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ya dade ya na addabar Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

Amurka ta ce, gwamnatoci da al’umma su na da rawar da za su taka domin ganin an hukunta ‘yan ta’adda tare da kare af’kuwar ayyukan ta’addanci.

Wata majiya ta ce, wannan sanarwa ta fito ne daga shafin hukumar shari’a ta kasar Amurka, mai amfani da harshen Faransanci a karkashin shirin bada kyauta domin tabbatar da adalci.

Sai dai masana, sun ce ba a san dalilin da ya sa hukumar ta yi amfani da sashin ta na Faransanci ba wurin fitar da sanarwar amma ba, tmaimakon sa shi a na Turanci.

Leave a Reply