Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Amurka Ta Hana Wasu ‘Yan Siyasar Nijeriya Shiga Kasar Ta

Gwamnatin kasar Amurka,

Gwamnatin kasar Amurka,

Gwamnatin kasar Amurka, ta bada sanarwar gaugawa cewa ta haramta wa wasu ‘yan siyasar Nijeriya shiga kasar ta.

Karanta Wannan; Tattalin Arziki: Majalisar Dattawa Ta Ce Za A Shigo Da Kayan Noma Na Zamani Nijeriya

Sanarwar ta ce, gwamnatin ba za ta kara barin mutanen su shiga Amurka ba, sakamakon yunkurin su na kokarin yi wa dimokradiyya kafar-ungulu a lokacin zaben shekara ta 2019.

Amurka ta fitar da sanarwar ne ta ofishin Harkokin Kasashen Waje, cewa ta ware mutanen ne domin rawar da su ka taka watanni biyar da su ka gabata a lokacin zaben da ya gabata a Nijeriya.

Ta ce ‘yan siyasar sun aikata ba daidai ba, ta yadda su ka tattaka dimokradiyya da kuma danne hakkokin jama’a, kamar yadda Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Morgan Ortagus ya bayyana.

Exit mobile version