Home Labaru Amurka: Sakatariyar Tsaron Cikin Gida Ta Ajiye Aikinta

Amurka: Sakatariyar Tsaron Cikin Gida Ta Ajiye Aikinta

338
0
Kirstjen Nielsen, Sakatariyar Tsaron Cikin Gida Ta Amurka
Kirstjen Nielsen, Sakatariyar Tsaron Cikin Gida Ta Amurka

Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka, Kirstjen Nielsen wadda ta aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsaren shugaba Trump na hana bakin haure shiga Amurka ta ajiye aiki.

Ta bayyana lokacin da ta shafe ta na aiki a ma’aikatar tsaro a matsayin wani abin alfahari a gare ta.

Shugaba Trump, ya bayyana kwamishinan hukumar hana fasa kwauri da tsaron iyakokin Amurka, Kevin McAleenan a matsayin wanda zai rike mukamin kafin ya nada wani sabon sakataren.

Kirstjen Nielsen ce ta aiwatar da shirin nan mai cike da takardama na raba kananan yara da iyayensu da ke kokarin shiga Amurka. Ba ta dai bayyana wani dalili na ajiye aikin nata ba, amma ta ce “wannan ne lokacin da yafi dacewa in sauka daga mukamin”, kuma ta yi ikirarin cewa tsaro ya inganta a Amurka idan aka kwatanta da lokacin da ta kama aiki a ma’aikatar.