Ma’aikatar shari’ah ta kasar Amurka ta na tuhumi mutum 80 akasarinsu, ‘yan Najeriya bisa hannu kan wani gagarumin shirin hada baki don satar miliyoyin dala ta hanyar aikata damfara da kuma halasta kudin Haram.
Wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka, ya wallafa a shafin intanet, ta bayyana tuhuma 252 da aka yi a kan mutanen da ake zargi da ke aiki da wani gungun masu halasta kudin haram da ke da sansani a birnin Los Angeles.
Hukumar ta ce an gabatar da tuhume-tuhumen ne bayan jami’an tsaro a safiyar Alhamis sun kama mutum 14 a fadin Amurka, 11 daga cikinsu a birnin Los Angeles.
Biyu daga cikin wadanda ake zargin dama suna a hannun hukumomi bisa wasu zarge-zargen na daban,inda kuma aka kama daya daga cikinsu a farkon makon nan.
Sauran wadanda ake zargin na zama ne a kasashen ketare, kuma yawancinsu na zaune ne a Najeriya.
Zarge-zargen dai sun hada da cewa mutanen guda 80 da wasu da ke da alaka da su suna amfani da hanyoyin damfara daban-daban.
Hanyoyin da suka hada da tura sakonnin email da sunan kasuwanci, da na soyayya, da kuma wadanda ake tura wa tsofaffi, inda sukan damfari mutane miliyoyin dala.