Home Home Amsa Kira: Kungiyar Ma’aikatan Lantarki Ta Najeriya Za Ta Shiga Yajin Aiki...

Amsa Kira: Kungiyar Ma’aikatan Lantarki Ta Najeriya Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Mai

89
0

Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta sanar da matakin tsunduma yajin aiki sakamon cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, lamarin da ta ce ya haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasa.

Shugaban ƙungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa BBC cewa ƙungiyar za ta shiga yajin aikin ne daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matuƙar gwamnati ba ta janye matakin cire tallafin man ba.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sannun muƙaddashin sakataren ƙungiyar na ƙasa Dominic Igwebike, ta yi kira ga ‘ya’yan ta su yi biyayya ga matakin ƙungiyar na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

Leave a Reply