Jam’iyyar PRP, ta ce ta dakatar da shugaban ta na jihar Taraba Abdullahi Maikasuwa na tsawon watanni uku bisa laifin rashawa da cin amanar jam’iyya.
Shugabannin jam’iyyar PRP a karkashin jagorancin Samuel Emmanuel, sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da su k araba wa manema labarai a birnin Jalingo na jihar Taraba..
Samuel Emmanuel ya ce sun tattauna, sun kuma yanke shawarar nada Injiniya Idris Umar a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar Taraba har zuwa lokacin da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya yanke hukunci dangane da dakatarwar.
Shugabannin jam’iyyar sun ce a lokuta da dama, Maikasuwa ya aikata rashawa da ayyukan cin amanar jam’iyya, inda ya rika yi wa ‘yan jam’iyyar barazana ya na karbar kudi daga hannun su.