Shugaban hukumar kula da muhalli ta jihar Bauchi Ibrahim Kabir, ya ce ambaliyar ruwan sama ta rusa gidaje dubu 1 da 453, sannan mutane 3 daga kananan hukumomin Zaki da Gamawa sun rasu.
Ibrahim Kabir ya bayyana haka ne, yayin da ya ke sanar wa gwamnan jihar Bala Mohammed ibtila’in da ya samu mutane a wadannan kananan hukumomi, inda ya ce ambaliyar ta rusa gadar da ke hada kauyukan kananan hukumomi biyu da wasu garuruwa a jihar.
Ya ce mutanen yankin su na bukatar kwalekwale 14 da za su rika amfani da su domin ci-gaba da harkokin su, sannan ya yi kira ga waɗanda ambaliyar ta shafa su gaggauta neman mafaka domin samun kariya.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan wadanda su ka rasa ‘yan’uwan su sakamakon ambaliyar.