Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta ce akalla mutane 49 ne, suka rasu a Arewa Maso Gabas, a sanadin mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa.
Kakakin hukumar, Manzo Ezekiel ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa inda ya bayyana cewa jihohin Adamawa da Taraba na yankin ne da kuma Jigawa lamarin ya fi shafa, inda mutum sama da 41,344 suka rasa matsuguninsu.
Kawo yanzu ambaliyar ta lalata gonalki masu fadin hekta 693 yayin da ake fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci.














































