Home Labarai Ambaliya da Zaizayar Ƙasa: Shettima ya ce Tinubu ya ba Jihohi Naira...

Ambaliya da Zaizayar Ƙasa: Shettima ya ce Tinubu ya ba Jihohi Naira Biliyan 108

31
0
download (1)
download (1)

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 108 ga jihohi 36 na Najeriya domin yaƙi da ambaliya da sauran nau’ukan bala’o’i.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba.

Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasa ya nuna niyyar sa ta haduwa da jihohi domin magance irin waɗannan matsaloli, ya ce ba a daɗe ba ya amince a ba kowace jiha Naira biliyan uku domin magance irin waɗannan matsalolin.

 Mataimakin Shugaban kasan ya ce da yardan ALLAH komai zai wuce kuma mutane za su koma garuruwan su, su cigaba da rayuwar su kamar yadda suka saba kamar babu abun da ya faru.

Leave a Reply