Home Home Amarya Ta Kashe Angonta A Bauchi

Amarya Ta Kashe Angonta A Bauchi

99
0

‘Yan sanda su na gudanar da bincike a kan wata matar aure da ta kashe mijin ta a jihar Bauchi

Idan dai ba a manta ba, rahotanni sun ruwaito yadda wata amarya mai suna Maimuna Suleiman ta kashe mijin ta Aliyu Muhammad ta hanyar daɓa ma shi wuƙa a kahon zuciya unguwar Ƙofar Ɗumi da ke Bauchi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauci Aminu Gimba Ahmed ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a Unguwar Kofar Dumi, inda wata mata mai mai suna Maimuna ‘yar shekaru 21 ta caka wa mijin ta wuka.

Rundunar ta ce bayan ta samu kiran gaugawa a kan lamarin, nan take jami’an ta su ka kama matar da ake zargi da kashe mijini ta.

Binciken wucin gadi ya nuna cewa, wadda ake zargin ta caka wa mijin ta wuka ne bayan rashin jituwa da su ka samu a gidan su na aure, sai dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Auwal Musa Mohammad ya bada umarnin a maida binciken Sashen Binciken Manyan Laifuffuka domin ci-gaba da bincike.

Leave a Reply