Home Labaru Amaechi Ya Fede Biri Har Wutsiya

Amaechi Ya Fede Biri Har Wutsiya

542
0
Rotimi Amaechi, Ministan sufuri
Rotimi Amaechi, Ministan sufuri

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce Najeriya kasa ce da ba a damu da bin doka ba, dan haka ‘yan Najeriya basu ganin laifin ‘yan siyasa akan matsalar talaucin da suke ciki.

Amaechi, ya ce ya san ‘yan siyasar da kafin su samu mulki basu da ko sisin kobo, amma da hawar su mulki suka mayar da kan su hamshakan masu kudi.

Da yake magana a wajen wani taro da aka yi akan matasan ‘yan siyasa masu tasowa a jihar Legas, Amaechi, ya ce akwai bukatar ‘yan siyasa su bayyana yadda suke son fitar da mutane daga cikin kangin talaucin da suke ciki.

Ya ce ya san ‘yan siyasar da suka saci makudan kudade suka azurta kansu, kuma wannan kudade da suka sata kamata ya yi ayi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran ayyukan more rayuwa ga al’umma. 

Ya cigaba da cewa kamata yayi ‘yan siyasar mu su fito karara su bayyanawa al’umma hanyoyin da zasu bi su fitar dasu daga cikin wannan kangin talaucin da suke ciki.

Leave a Reply