Home Labaru Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga

833
0
Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga
Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Al’umomin jihar Zamfara, sun koka da yadda mahara ke ci-gaba da kai hare-hare, duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ta cimmawa da su.

Mazauna kauyukan Dankurmi da Zargado da Danhayin Zargado da Farar Kasa da ke masarautar Dan-sadau a karamar hukumar Maru, sun ce maharan su na dauke ne da manyan makamai, inda su ke cin Karen su ba babbaka a yankunan.

Rahotanni sun ce a cikin kwanaki biyu maharan sun kwashe shanu sama da 600 a kauyaen Dan-kurmi, baya ga kashe mutune biyu da likitan da ke kula da al’ummar kauyen.

Rahoton ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kashe wani shugaban kungiyar ‘yan sa-kai a kauyen Dan ma’aji, tare da harbin wani dan kungiyar mai suna Bataliya a kauyen Farar Kasa, wanda a ka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar SP Muhammad Shehu, ya ce su na daukar matakan da su ka dace don kawo karshen matsalolin, ya na mai cewa wannan ba matsalar da za a magance a dare daya ce ba.

Leave a Reply