Wasu al’ummomi mazauna iyakokin Nijeriya da Nijar, sun fara nuna fargaba a kan abin da ka iya zama illa gare su muddin ba a warware tankiyar juyin mulkin da aka yi cikin ruwan sanyi ba.
Tuni dai masu sharhi a kan al’amurran tsaro sun fara bada shawara a kan daukar matakai na tsirar da mazauna iyakokin kasashen biyu.
Kamar dai yadda kasashe bakwai na Afirka ke da iyakoki da Jamhuriyar Nijar, haka ma Nijeriya ta na da iyakoki da ita a jihohi bakwai, wadanda su ka hada da Borno da Yobe da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.
Mazauna iyakokin sun ce, duk abin da ya shafi Nijar su ma ya shafe su, duba da yadda su ke hulda da kasar cikin lumana da ‘yan’uwantaka. Tankiyar da ke tsakanin jagororin mulkin sojin kasar Nijar da Kungiyoyin Kasashen Afrika da ma wasu na duniya ta fara jefa fargaba a zukatan al’ummomin da ke makwabtaka da Nijar, kamar yadda wasu mazauna Kamba ta jihar Kebbi da Illela ta jihar Sokoto ke nuna fargaba