Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Almundahana: Hukumar EFCC Ta Kwace Naira Miliyan 643.9 Da Dala Miliyan 706.8 A 2019

Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC

Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC reshen jihar Kano ta kwace Naira miliyan 643 da dubu dari 942 daga hannun wasu barayin gwamnati

Shugaban hukumar Ibrahim Magu wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar mai kula da shiyyar kano Akaninyene Eziman ya bayyana haka a Kano.

Akaninyene ya ce hukumar ta gano Dala miliyan 706 da dubu dari 800 da wasu kudaden kasar Sin Yen dubu  2 da dari 800 da  kuma na saudiyya Riyal dari 294 da dari 950.

Sannan shugaban hukumar ya kara da cewa, sun samu korafe-korafe 495 wanda tuni suka karbi 325 daga ciki su, sannan sun shigar da kararraki 100 gaban kotu domin gudanar da bincike.

Magu ya cigaba da cewa, sun kuma samu kudaden ne a farkon watan Junairu zuwa watan Disamban na shekara ta 2019.

Ibarahim Magu ya ce yaki da rashin gaskiya aiki ne kowa, wanda hakan zai sa fidda Nijeriya daga halin ka-ka-ni-kayi, matakin da ya ce dole ne al’ummar su bada hadin kai domin yaki marasa kishin Nijeriya.

Exit mobile version